3 “Ra'ubainu, kai ɗan farinane, ƙarfina,Ɗan balagata, isasshe kuma, mafiƙarfi duka cikin 'ya'yana.
4 Kamar ambaliyar ruwa mai fushikake,Amma ba za ka zama mafi darajaba,Domin ka hau gadon mahaifinka,Sa'an nan ka ƙazantar da shi.
5 “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne,Suka mori takubansu cikin ta dahankali.
6 Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsuba,Gama cikin fushinsu suka kashemutane,Cikin gangancinsu kuma sukagurgunta bijimai.
7 La'ananne ne fushinsu domin maitsanani ne,Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce.Zan warwatsa su cikin dukan ƙasarYakubu,In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.
8 “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabeka,Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,'Yan'uwanka za su rusuna agabanka.
9 Yahuza ɗan zaki ne,Ya kashe ganima sa'an nan ya komowurin ɓuyarsa.Yahuza kamar zaki yake,Yakan kwanta a miƙe,Ba mai ƙarfin halin da zai tsokaneshi.