9 Yahuza ɗan zaki ne,Ya kashe ganima sa'an nan ya komowurin ɓuyarsa.Yahuza kamar zaki yake,Yakan kwanta a miƙe,Ba mai ƙarfin halin da zai tsokaneshi.
10 Yana riƙe da sandan mulkinsa,Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,Har Shilo ya zo.Zai mallaki dukan jama'o'i.
11 Zai ɗaure aholakinsa a kurangarinabi,A kuranga mafi kyau,Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,Ruwan inabi ja wur kamar jini.
12 Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.
13 “Zabaluna zai zauna a gefen teku,Zai zama tashar jiragen ruwa,Kan iyakarsa kuma zai kai harSidon.
14 “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,Ya kwanta a miƙe tsakaninjakunkunan shimfiɗa.
15 Saboda ya ga wurin hutawa ne maikyau,Ƙasar kuma mai kyau ce,Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa dominɗaukar kaya,Ya zama bawa, yana yin aiki maiwuya.