13 Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.
14 Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.
15 Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba'in da biyar, tsayinsa ƙafa arba'in da biyar.
16 Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
17 Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.
18 Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da 'ya'yanka, da matarka, da matan 'ya'yanka tare da kai.
19 Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace.