13 Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama'ar shari'a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.
14 Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”
15 Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.
16 A sa'ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”
17 Amma surukin Musa ya ce, “Abin nan da kake yi ba daidai ba ne.
18 Kai da jama'an nan da suke tare da kai za ku rafke, saboda abin da kake yi ya fi ƙarfinka, kai kaɗai ba za ka iya ba.
19 Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama'a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi.