3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.
4 Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.
5 Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.
6 Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne.”
7 'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”
8 Sai Gimbiya ta ce mata, “Je ki.” Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn.
9 Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, “Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki.” Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa.