12 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13 “Kada ka yi kisankai.
14 “Kada ka yi zina.
15 “Kada ka yi sata.
16 “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.
17 “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”
18 Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa.