3 “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.
4 “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.
5 Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.
6 Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararrakin da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.
7 “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
8 “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.
9 Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida,