14 Amma idan mutum ya fāɗa wa ɗan'uwansa da niyyar kisankai, lalle, sai a kashe shi ko da ya gudu zuwa bagadena.
15 “Wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle, kashe shi za a yi.
16 “Wanda ya saci mutum, ya sayar, ko kuwa a iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.
17 “Wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle kashe shi za a yi.
18 “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya,
19 idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai.
20 “In mutum ya dūki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi.