3 Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa'ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi.
4 Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa 'ya'ya mata ko maza, to, matar da 'ya'yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.
5 Amma idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da 'ya'yansa, ba ya son 'yancin,
6 to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa'an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.
7 “Idan mutum ya sayar da 'yarsa kamar baiwa, ba za a 'yanta ta kamar bawa ba.
8 Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.
9 Idan ya ba da ita ga ɗansa ne sai ya maishe ta kamar 'yarsa.