16 Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra'ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”
17 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
18 “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki.
19 A wurin ne Haruna da 'ya'yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu.
20 Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.
21 Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”
22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,