14 Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.
15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
16 Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.
17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.
18 Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.
19 A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni.
20 A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni.