2 Sai Ubangiji ya ce mini,“Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna,Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.
3 Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa,Yana gaggautawa zuwa cikarsa,Ba zai zama ƙarya ba.Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri,Hakika zai zo, ba zai makara ba.
4 Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi,Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.
5 “Ruwan inabi kuma yana yaudarar mai fariya,Don haka ba ya zama a gida.Haɗamarsa tana da fāɗi kamar Lahira,Kamar kuma mutuwa yake, ba ya ƙoshi.Ya tattara wa kansa al'ummai duka,Ya kwaso wa kansa mutane duka.”
6 “Ai, waɗannan duka za su yi ta yi masa zambo,Su yi masa dariya ta raini,Su ce, ‘Tasa ta ƙare, shi wanda ya tattara abin da ba nasa ba,Har yaushe zai riƙa arzuta kansa ta hanyar ba da rance?’
7 Mabartanka za su tasar maka nan da nan,Waɗanda suke binka bashi za su farka.Za ka zama ganima a gare su.
8 Saboda ka washe al'umman duniya da yawa,Sauran mutanen duniya duka za su washe ka,Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya,Da birane, da mazauna a cikinsu.