1 Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,
2 wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,
3 da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.
4 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
5 “Na san ka tun kafin a yi cikinka,Na keɓe ka tun kafin a haife ka,Na sa ka ka zama annabi gaal'ummai.”
6 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!Ban san abin da zan faɗa ba,Gama ni yaro ne.”