Irm 18 HAU

Irmiya a Gidan Maginin Tukwane

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2 “Ka tashi, ka gangara zuwa gidan maginin tukwane, a can zan yi maka magana.”

3 Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, na iske shi yana ginin tukwane a kan na'urar ginin tukwanen.

4 Abin da yake ginawa ya lalace a hannunsa, sai ya sāke gina wani abu dabam da yumɓu ɗin, yadda ya ga dama.

5 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,

6 “Ya jama'ar Isra'ila, ashe, ba zan yi da ku kamar yadda maginin tukwanen nan ya yi ba? Duba, kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya ku jama'ar Isra'ila.

7 A duk lokacin da na ce zan tumɓuke, in kakkarya in hallaka wata al'umma, ko wani mulki,

8 idan wannan al'umma da na yi magana a kanta, ta juyo, ta tuba daga mugayen ayyukanta, zan janye masifar da na yi niyyar aukar mata.

9 A duk kuma lokacin da na ce zan gina, in kafa wata al'umma, ko wani mulki,

10 amma idan al'ummar ta aikata mugunta a gabana, ta ƙi saurarawa ga maganar, zan janye alherin da na yi niyyar yi mata.

11 Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’

12 Amma za su ce, ‘Wannan ba abin da za mu kula da shi ba ne, mu ra'ayinmu za mu bi, kowannenmu kuwa zai yi bisa ga nufin tattaurar muguwar zuciyarsa.’

13 “Domin haka ni Ubangiji na ce,‘Ka tambayi sauran al'umma.Wa ya taɓa jin irin wannan?Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abuƙwarai!

14 Dusar ƙanƙara mai danshi ta taɓarabuwa da tsaunukan Lebanon?Ko ruwan rafuffuka mai sanyi na kandutse ya taɓa ƙonawa?

15 Amma mutanena sun manta da ni,Sun ƙona wa gumaka turare.Sun yi tuntuɓe a cikin al'amuransu,a hanyoyin dā,Sun bi ɓarayin hanyoyi, ba su bikarauka ba.

16 Sun mai da ƙasarsu abarbanƙyama,Abin raini har abada.Duk wanda ya wuce ta wurin zairazana ya kaɗa kansa.

17 Haka zan warwatsa suKamar yadda iskar gabas take yi, agaban abokan gābansu,Zan juya musu baya, ba za su gafuskata ba,A ranar masifarsu.’ ”

Maƙarƙashiyar Mutane da Addu'ar Irmiya

18 Sa'an nan suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya, gama firist ba zai bar bin shari'a ba. Haka nan ma masu hikima ba za su bar yin shawara ba, haka nan kuma annabi ba zai bar yin magana ba! Ku zo mu kai ƙararsa, kada mu kula da abin da zai faɗa.”

19 Irmiya kuwa ya yi addu'a ya ce,“Ya Ubangiji, ka kasa kunne gare ni,ka ji ƙarar maƙiyana!

20 Daidai ne a rama alheri damugunta?Duk da haka sun kafa wa raina tarko.Ka tuna yadda na tsaya a gabanka,Na yi maganar alheri a kansu,Domin ka janye fushinka daga garesu.

21 Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansuyunwa,Ka bashe su ga takobi,Bari matansu su rasa 'ya'ya,mazansu su mutu,Ka sa annoba ta kashe mazansu,A kashe samarinsu da takobi ayaƙi.

22 Bari a ji kururuwa daga gidajensu,Saboda maharan da ka aika musufarat ɗaya,Gama sun haƙa rami don in fāɗa,Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.

23 Amma ya Ubangiji,Ka san dukan maƙarƙashiyarsu,su kashe ni,Kada ka gafarta musu muguntarsu,kada kuma ka shafe zunubinsudaga gabanka.Ka sa a jefar da su daga gabanka,Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”