Irm 36 HAU

An Ƙone Littafi

1 A sa'ad da Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, yana shekara huɗu da sarauta, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

2 “Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.

3 Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”

4 Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya.

5 Sai Irmiya ya umarci Baruk, ya ce, “An hana ni zuwa Haikali,

6 saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda take a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu.

7 Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”

8 Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya umarce shi. Ya karanta takardan nan ta maganar Ubangiji a Haikalin Ubangiji.

9 A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama'ar Urushalima da dukan jama'ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji.

10 Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda take a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11 Sa'ad da Mikaiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji da take a littafin,

12 sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna.

13 Sai Mikaiya ya faɗa musu dukan maganar da ya ji sa'ad da Baruk ya karanta littafin a kunnuwan jama'a.

14 Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama'a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu.

15 Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu.

16 Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.”

17 Suka kuma tambayi Baruk, suka ce, “Ka faɗa mana yadda ka yi ka rubuta wannan magana. Ya yi maka shibta ne?”

18 Sai Baruk ya ce musu, “Ya yi mini shibtar dukan wannan magana ne, na kuwa rubuta su da tawada a takarda.”

19 Sarakunan kuwa suka ce wa Baruk, “Ka tafi, da kai da Irmiya ku ɓuya kada ku bari kowa ya san wurin da kuke.”

20 Suka tafi zauren sarki bayan sun ajiye littafin a ɗakin Elishama, magatakarda, suka sanar da sarki dukan abin da yake cikin littafin.

21 Sarki ya aiki Yehudi ya je ya kawo littafin. Sai ya je ya ɗauko littafin daga ɗakin Elishama magatakarda. Yehudi kuwa ya karanta wa sarki tare da dukan sarakunan da suke tsaye kewaye da sarkin.

22 A watan tara ne, sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, ga wuta tana ci cikin kasko a gabansa.

23 Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka.

24 Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.

25 Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.

26 Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!

27 Bayan da sarki ya ƙone littafin da Baruk ya rubuta ta wurin shibtar da Irmiya ya yi masa, sai Ubangiji ya yi wa Irmiya magana, ya ce,

28 ya ɗauki wata takarda ya rubuta dukan maganar da take cikin littafin da Yehoyakim Sarkin Yahuza, ya ƙone.

29 Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’

30 Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.

31 Zan hukunta shi, shi da zuriyarsa, da barorinsa saboda muguntarsu. Zan kawo dukan masifar da na hurta a kansu, da a kan mazaunan Urushalima, da a kan mutanen Yahuza, amma sun ƙi ji.”

32 Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.