Irm 51 HAU

Hukuncin Ubangiji a kan Babila

1 Ubangiji ya ce,“Ga shi, zan kawo iskar ɓarna akan BabilaDa mazaunan Kaldiya.

2 Zan aika da masu casawa zuwaBabila, za su casa ta,Su bar ƙasarta kango.Za su kewaye ta a kowane sashiA wannan ranar masifa.

3 Kada ku bar maharbi ya yi harbi dabakansa,Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,Kada ku rage samarinta,Ku hallaka dukan sojojinta.

4 Za su fāɗi matattu a ƙasarKaldiyawa,Za a sassoke su a titunansu.”

5 Allah na Isra'ila da Yahuza,Ubangiji Mai Runduna, bai yashesu ba,Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki naIsra'ila zunubi.

6 Ku gudu daga cikin Babila,Bari kowa ya ceci ransa,Kada a hallaka ku tare da ita,Gama a wannan lokaci Ubangiji zaisāka mata,Zai sāka mata bisa ga alhakinta.

7 Babila ta zama ƙoƙon zinariya ahannun Ubangiji,Ta sa dukan duniya ta yi maye.Ƙasashen duniya sun sha ruwaninabinta, suka haukace.

8 Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, takakkarye,Ku yi kuka dominta!Ku samo mata magani domin azabarda take sha, watakila ta warke.

9 Mun ba Babila magani, amma ba tawarke ba.Bari mu ƙyale ta, kowannenmu yakoma garinsu,Gama hukuncinta ya kai sammai, yayi tsawo har samaniya.

10 Ubangiji ya baratar da mu a fili,Bari mu tafi mu yi shelar aikinUbangiji Allahnmu a cikinSihiyona.

11 Ku wasa kibau, ku cikakwaruruwanku!Ubangiji ya ta da ruhun sarakunanMediyawa,Domin yana niyyar hallaka Babila.Gama Ubangiji zai yi ramuwasaboda Haikalinsa.

12 Ku ta da tuta don a faɗa wa garunBabila,Ku ƙarfafa matsara,Ku sa su su yi tsaro,Ku kuma sa 'yan kwanto!Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwaaikataAbin da ya faɗa a kan mazaunanBabila.

13 Ƙarshenki ya zo,Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa,Mai yawan dukiya.Ajalinki ya auka.

14 Ubangiji Mai Runduna ya rantse dazatinsa, ya ce,“Hakika zan cika Babila da mutanekamar fāra,Za su kuwa raira waƙar nasara akanta.”

15 Ubangiji ne ya halicci ƙasa daikonsa,Ya kafa duniya da hikimarsa,Ya kuma shimfiɗa sammai dafahiminsa.

16 Bisa ga umarninsa ruwan da yakesamaniya yakan yi ruri,Yakan sa gajimare su tashi dagaƙarshen duniya,Yakan sa walƙiya ta walƙata cikinruwan sama,Yakan sa iska ta haura daga cikintaskokinsa.

17 Kowane ɗan adam wawa ne, mararilimi,Kowane maƙerin zinariya kuma zaisha kunya daga wurin gumakansa,Gama siffofinsa na ƙarya ne, banumfashi a cikinsu.

18 Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwane kawai,Za su lalace a lokacin da za ahukunta su.

19 Amma wanda yake wajen Yakubu bahaka yake ba,Domin shi ne ya halicci dukanabu,Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne,Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.

20 Ubangiji ya ce,“Kai ne guduma da kayan yaƙina,Da kai ne na farfasa ƙasashenduniya,Da kai ne na hallaka mulkoki.

21 Da kai ne na karya doki damahayinsa,

22 Da kai ne na farfasa karusa damahayinsa.Da kai ne na kakkarya mace danamiji,Da kai ne na kakkarya tsoho dasaurayi,Da kai ne na kakkarya saurayi dabudurwa,

23 Da kai ne na kakkarya makiyayi dagarkensa,Da kai ne na kakkarya manoma dadawakan nomansa,Da kai ne na kakkarya masu mulkida shugabanni.”

24 Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.

25 Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse maihallakarwa,Wanda ya hallaka duniya duka.Zan miƙa hannuna gāba da kai,Zan mirgino da ƙasa dagaƙwanƙolin dutse,Zan maishe ka ƙonannen dutse.

26 Ba za a sami dutsen yin kusurwa, kona kafa harsashen gini a cikinkaba,Amma za ka zama marar amfani harabada.”

27 Ku ta da tuta a duniya,Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙida ita,Ku kirawo mulkokin Ararat, da naMinni, da na Ashkenaz, su yi yaƙida ita.Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zaishugabanci yaƙin da za a yi da ita,Ku kawo dawakai kamar fāra.

28 Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,Sarakunan Mediyawa, da masumulkinsu, da shugabanninsu,Da kowace ƙasar da take ƙarƙashinmulkinsu.

29 Duniya ta girgiza, tana makyarkyatasaboda azaba,Gama nufin Ubangiji na gāba daBabila ya tabbata,Nufinsa na mai da ƙasar Babilakufai, inda ba kowa.

30 Sojojin Babila sun daina yaƙi, sunazaune a cikin kagaransu.Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,An sa wa wuraren zamanta wuta,An karya ƙyamaren ƙofofingarinta.

31 Maguji yana biye da maguji a guje,Jakada yana biye da jakada,Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewaan ci birninsa a kowane gefe.

32 An ƙwace mashigaiAn ƙone fadamu da wuta,Sojoji sun gigice.

33 Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah naIsra'ila na ce,“Mutanen Babila sun zama kamardaɓen masussukaA lokacin da ake sussuka,Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbeta zai zo.”

34 Nebukadnezzar, Sarkin Babila, yacinye Urushalima,Ya ragargaza ta,Ya maishe ta kufai,Ya haɗiye ta kamar yadda dodonruwa yakan yi,Ya cika cikinsa da kayanmarmarinta,Ya tatse ta sarai.

35 Bari mutanen Sihiyona su ce,“Allah ya sa muguntar da mutanenBabila suka yi mana ta komakansu!”Bari kuma mutanen Urushalima suce,“Allah ya sa hakkin jininmu ya komakan Kaldiyawa!”

36 Ubangiji ya ce,“Zan tsaya muku,Zan ɗaukar muku fansa,Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu suƙafe.

37 Babila za ta zama tarin juji, wurinzaman diloli,Abar ƙyama da abar ba'a, inda bakowa.

38 Mutanen Babila za su yi ruri kamarzakuna,Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.

39 Sa'ad da suke cike da haɗama zan yimusu biki,In sa su sha, su yi maye, su yimurna.Za su shiga barcin da ba za su farkaba.

40 Zan kai su mayanka kamar 'yanraguna, da raguna, da bunsurai.

41 “An ci Babila,Ita wadda duniya duka take yabo ancinye ta da yaƙi,Ta zama abar ƙyama ga sauranal'umma!

42 Teku ta malalo a kan Babila,Raƙuman ruwa masu hauka sunrufe ta.

43 Garuruwanta sun zama abinƙyama,Ta zama hamada, inda ba ruwa,Ƙasar da ba mazauna,Ba kuma mutumin da zai ratsa tacikinta.

44 Zan hukunta Bel, gunkin Babila,Zan sa ya yi aman abin da yahaɗiye,Ƙasashen duniya ba za su ƙarabumbuntowa wurinsa ba.Garun Babila ya rushe!”

45 “Ku fito daga cikinta, ya jama'ata,Kowa ya tsere da ransa daga zafinfushin Ubangiji.

46 Kada zuciyarku ta yi suwu,Kada kuma ku ji tsoro sabodalabarin da ake ji a ƙasar,Labari na wannan shekara dabam,na wancan kuma dabam,A kan hargitsin da yake a ƙasar,Mai mulki ya tasar wa mai mulki.

47 Saboda haka kwanaki suna zuwa,Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila,Za a kunyatar da dukan ƙasarBabila,Dukan matattunta za su faɗi atsakiyarta.

48 Sa'an nan sama da duniya, da dukanabin da take cikinsu,Za su raira waƙar farin ciki,Domin masu hallakarwa daga arewada za su auko mata,Ni Ubangiji na faɗa.”

49 Babila za ta fāɗi,Saboda mutanen Isra'ila da dukanmutanen duniya waɗanda takashe.

50 Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!Ku gudu! Kada ku tsaya!Ku tuna da Ubangiji a can nesa indakuke,Ku kuma yi ta tunawa daUrushalima.

51 Mun sha kunya saboda zargin da akeyi mana,Kunya ta rufe mu,Gama baƙi sun shiga tsarkakanwurare na Haikalin Ubangiji.

52 “Domin haka kwanaki suna zuwa,”in ji Ubangiji,“Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila, da dukan ƙasarta,Waɗanda aka yi wa rauni, za su yinishi.

53 Ko da Babila za ta hau samaniya,Ta gina kagara mai ƙarfi a can,Duk da haka zan aiki masuhallakarwa a kanta,Ni Ubangiji na faɗa.”

54 Ku ji muryar kuka daga Babila,Da hargowar babbar hallakarwadaga ƙasar Kaldiyawa!

55 Gama Ubangiji yana lalatar daBabila,Yana kuma sa ta kame bakinta naalfarma,Sojoji suna kutsawa kamar raƙumanruwa,Suna ta da muryoyinsu.

56 Gama mai hallakarwa ya auka waBabila,An kama sojojinta,An kuma kakkarya bakunansu,Gama Ubangiji shi Allah ne, maisakayya,Zai yi sakayya sosai.

57 “Zan sa mahukuntanta, da masuhikimarta,Da masu mulkinta, dashugabanninta,Da sojojinta su sha su yi maye.Za su dinga yin barcin da ba za sufarka ba,”In ji Sarkin, mai suna Ubangiji MaiRunduna.

58 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,Za a baje garun nan na Babila maifāɗiZa a kuma ƙone dogayenƙyamarenta da wuta.Mutane sun wahalar da kansu abanza.Sauran al'umma sun yi wahala kawaidomin wutar lalata.”

59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.

60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila.

61 Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan.

62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’

63 Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis.

64 Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ”Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.