6 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!Ban san abin da zan faɗa ba,Gama ni yaro ne.”
7 Amma Ubangiji ya ce mini,“Kada ka ce kai yaro ne,Kai dai ka tafi wurin mutanen da zanaike ka,
8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare dakai,Zan kiyaye ka.Ni Ubangiji na faɗa.”
9 Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,“Ga shi, na sa maganata a bakinka.
10 Ga shi, a wannan rana na ba ka iko akan al'ummai da mulkoki,Don ka tumɓuke, ka rusar,Ka hallakar, ka kaɓantar,Ka gina, ka dasa.”
11 Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”
12 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”