8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare dakai,Zan kiyaye ka.Ni Ubangiji na faɗa.”
9 Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,“Ga shi, na sa maganata a bakinka.
10 Ga shi, a wannan rana na ba ka iko akan al'ummai da mulkoki,Don ka tumɓuke, ka rusar,Ka hallakar, ka kaɓantar,Ka gina, ka dasa.”
11 Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”
12 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”
13 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?”Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”
14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar.