1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya cewa,
2 “Ka ji maganar wannan alkawari, sa'an nan ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.
3 Ka faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, la'ananne ne wanda bai kula da maganar alkawarin nan ba.
4 Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.
5 Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ”Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”
6 Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata.