1 Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,
2 “Yahuza tana makoki,Ƙofofin biranenta suna lalacewa,Mutanenta suna kwance a ƙasa,suna makoki,Urushalima tana kuka da babbarmurya.
3 Manyan mutanenta sun aikibarorinsu su ɗebo ruwa.Da suka je maɓuɓɓuga, sai sukatarar ba ruwa.Sai suka koma da tulunansuhaka nan,An kunyatar da su, an ƙasƙantarda su,Suka lulluɓe kansu don kunya.
4 Saboda ƙasar ta bushe,Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,Manoma sun sha kunya,Suka lulluɓe kansu don kunya.
5 Barewa ma a saura takan gudu,Ta bar ɗanta sabon haihuwa,Domin ba ciyawa.