12 Kursiyi mai daraja,Da aka sa a bisa tun daga farko,Wurin ke nan inda Haikalinmuyake.
13 Ya Ubangiji, begen Isra'ila,Duk waɗanda suka rabu da kai, za susha kunya.Waɗanda suka ba ka baya a duniyaza a rubuta suDomin sun rabu da Ubangiji,maɓuɓɓugar ruwan rai.
14 Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwawarke,Ka cece ni, zan kuwa cetu,Gama kai ne abin yabona.
15 Ga shi, suna ce mini,“Ina maganar Ubangiji take?Ta zo mana!”
16 Amma ni ban yi gudun zamanmakiyayi a gabanka ba,Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba,Ka kuwa sani.Abin da ya fito daga bakina kuwa,A bayyane yake gare ka.
17 Kada ka zamar mini abin razana,Kai ne mafakata cikin ranar masifa,
18 Bari waɗanda suka tsananta mini susha kunya,Amma kada ka bar ni in kunyata.Bari su tsorata,Amma kada ka bar ni in tsorata.Ka aukar musu da ranar masifa,Ka hallaka su riɓi biyu!