3 Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.
4 Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”
5 Ubangiji ya ce,“La'ananne ne mutumin da yakedogara ga mutum,Wanda jiki ne makaminsa,Wanda ya juya wa Ubangiji baya,
6 Gama yana kama da sagagi ahamada,Ba zai ga wani abu mai kyau yanazuwa ba.Zai zauna a busassun wurarenhamada,A ƙasar gishiri, inda ba kowa.
7 “Mai albarka ne mutumin da yakedogara ga Ubangiji,Wanda Ubangiji ne madogararsa.
8 Shi kamar itace ne wanda ake dasa abakin rafiWanda yake miƙa saiwoyinsa zuwacikin rafin,Ba zai ji tsoron rani ba,Kullum ganyensa kore ne,Ba zai damu a lokacin fari ba,Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.
9 “Zuciya ta fi kome rikici,Cuta gare ta matuƙa,Wa zai san kanta?