11 Akwai wata al'umma da ta taɓasāke gumakantaKo da yake su ba kome ba ne?Amma mutanena sun sauya darajarsuda abin da ba shi da rai.
12 Sammai, ku girgiza saboda wannan,ku razana,Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.
13 Mutanena sun yi zunubi iri biyu,Sun rabu da ni, ni da nakemaɓuɓɓugar ruwan rai,Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,hudaddu,Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.
14 “Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kumahaife shi bawa ba,Amma me ya sa ya zama ganima?
15 Zakuna suna ruri a kansa,Suna ruri da babbar murya.Sun lalatar da ƙasarsa,Garuruwansa sun lalace,Ba wanda yake zaune cikinsu.
16 Mutanen Memfis kuma da naTafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.
17 Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kankawannan,Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,Sa'ad da ya bishe ka a hanya.