3 Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji,Nunar fari ta girbina.Dukan waɗanda suka ci daga cikinkisun yi laifi,Masifa za ta auko miki.Ni Ubangiji, na faɗa.”
4 Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.
5 Ubangiji ya ce,“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,Da suka bar bina?Suka bauta wa gumaka marasaamfani,Su kuma suka zama marasa amfani.
6 Ba su kula da ni ba,Ko da yake na cece su daga ƙasarMasar.Na bi da su a cikin hamada,A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,Busasshiya mai yawan hatsari,Ba a bi ta cikinta,Ba wanda yake zama cikinta kuma.
7 Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,Don su more ta su ci amfaninta,Amma da suka shiga, sun ƙazantarmini da ita,Suka sa ƙasar da na gādar musu tazama abar ƙyama.
8 Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina UbangijiYake?’ ba.Masanan shari'a ba su san ni ba.Masu mulki sun yi mini laifi,Annabawa sun yi annabci da sunanBa'al,Sun bi waɗansu abubuwa marasaamfani.”
9 “Domin haka, ni Ubangiji zangabatar da ku gaban shari'a,Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan'ya'yanku, wato jikokinku.