31 Ya ku mutanen zamanin nan, kusaurari maganata.Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasarda take da kurama?Don me fa mutanena suke cewa,‘Mu 'yantattu ne,Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32 Budurwa ta manta da kayankwalliyarta?Ko kuwa amarya ta manta da kayanadonta?Amma mutanena sun manta da nikwanaki ba iyaka.
33 Kun sani sarai yadda za ku yi kufarauci masoya,Har mugayen mata ma, kun koyamusu hanyoyinku.
34 Tufafinku sun ƙasantu da jininmarasa laifi,Waɗanda ba ku same su suna fasagidajenku ba.Amma duk da haka kuna cewa,
35 ‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.
36 Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,Sai ku yi nan ku yi can?Masar za ta kunyata ku kamar yaddaAssuriya ta yi.
37 Da hannuwanku a kā za ku komodaga Masar don kunya.Gama waɗanda kuke dogara gare su,ni Ubangiji, na ƙi su,Ba za ku yi arziki tare da su ba.”