6 Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”
7 “Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwaruɗu,Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni.Na zama abin dariya dukan yini,Kowa yana ta yi mini ba'a.
8 Duk lokacin da zan yi magana,Nakan ta da murya in yi magana daƙarfi cewa,‘Hargitsi da hallakarwa!’Gama saboda maganar Ubangiji nazama abin zargi,Da abin ba'a dukan yini.
9 Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangijiba,Ban zan ƙara yin magana da sunansaba,’Sai in ji damuwa a zuciyata,An kulle ta a ƙasusuwana,Na gaji da danne ta a cikina,Ba zan iya jurewa ba.
10 Na ji mutane da yawa suna sa minilaƙabi cewa,‘Razana ta kowace fuska,’Suna cewa, ‘Mu la'anta shi!Mu la'anta shi!’Har ma da abokaina shaƙiƙaiSuna jira su ga fāɗuwata.Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi,Sa'an nan ma iya rinjayarsaMu ɗauki fansa a kansa.’
11 Amma Ubangiji kana tare da niKamar jarumi mai bantsoro,Don haka masu tsananta mini za suyi tuntuɓe,Ba za su rinjaye ni ba.Za su sha kunya ƙwarai,Gama ba za su yi nasara ba.Ba za a manta da su ba.
12 Ya Ubangiji Mai Runduna, maigwada adali,Mai ganin zuciya duk da tunani,Ka sa in ga sakayyar da za ka yimusu,Gama a gare ka nake kawoƙarata.”