3 Sai Irmiya ya ce musu,
4 “Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.
5 Ni kaina zan yi yaƙi da kai da dukan ƙarfina, da hasalata, da dukan zafin fushina.
6 Zan kuwa kashe mazaunan birnin nan, mutum da dabba, da babbar annoba.
7 Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’
8 “Sai ka faɗa wa wannan jama'a, ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku.
9 Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa.