1 Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.
2 A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.
3 Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?”Sai na ce, “'Ya'yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”
4 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,
5 “Haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, kamar kyawawan ɓauren nan, haka nake ganin mutanen Yahuza waɗanda aka kai su bautar talala a ƙasar Kaldiyawa.