17 Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai?
18 Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.
19 Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,
20 wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.
21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,
22 ‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa'an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.’ ”