1 Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce,
2 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Na karya karkiyar Sarkin Babila.
3 Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila.
4 Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”
5 Sa'an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama'ar da suke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce,