10 Sai annabi Hananiya ya cire karkiyar daga wuyan annabi Irmiya ya karya ta.
11 Sa'an nan Hananiya ya yi magana a gaban dukan jama'a, ya ce, “In ji Ubangiji, haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, daga wuyan dukan al'ummai kafin shekara biyu.” Sai annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.
12 Da ɗan daɗewa bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar da take a wuyan annabi Irmiya, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce
13 ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta.
14 Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”
15 Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya.
16 Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”