10 “Ubangiji ya ce, ‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.
11 Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.
12 Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.
13 Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.
14 Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’
15 “Domin kun ce, Ubangiji ya ba ku annabawa a Babila,
16 ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama'ar da suke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba.