1 Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.”
2 Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar dasuka tsere wa takobi,Sun sami alheri a cikin jeji,A sa'ad da Isra'ila suka nemihutawa.”
3-4 Ubangiji ya bayyana gare ni tundaga nesa cewa,“Ya Isra'ila, budurwa!Na kusace ki da madawwamiyarƙaunata,Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata agare ki ba.Zan sāke gina ki,Za ki kuwa ginu,Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe,Za ki shiga rawar masu murna.
5 Za ki sāke dasa gonar inabiA kan duwatsun Samariya,Masu dashe za su dasa,Za su mori 'ya'yan.