15 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”
16 Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu'a ga Ubangiji, na ce,
17 “Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.
18 Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.
19 Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.
20 Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.
21 Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar.