18 Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”
19 Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa,
20 idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,
21 to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi.
22 Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”
23 Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,
24 “Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.