23 Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,
24 “Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.
25 Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da take mulkin sammai da duniya ba,
26 sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”