4 A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna.
5 Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.
6 Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce,
7 “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.
8 Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.
9 Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.
10 Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”