9 Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.
10 Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”
11 Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir'auna,
12 sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi.
13 A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”
14 Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni.
15 Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.