1 Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya yake faɗa wa dukan mutane cewa,
2 “Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi.
3 Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”
4 Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”
5 Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.”
6 Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.