1 Ubangiji ya ce,“Ya mutanen Isra'ila, idan za kujuyo ku komo wurina,Idan kuka kawar da abubuwanbanƙyama daga gabana,Kuka kuma bar yin shakka,
2 Idan kun yi rantsuwa kuka ce,‘Har da ran Ubangiji kuwa,‘Da gaskiya, da aminci, da adalci,Sa'an nan sauran al'umma za su soin sa musu albarka,Za su kuma yabe ni.”
3 Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,“Ku kafce saurukanku,Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.
4 Ya ku mutanen Yahuza da naUrushalima,Ku yi wa kanku kaciya dominUbangiji,Ku kawar da loɓar zukatankuDon kada fushina ya fito kamarwuta,Ya cinye, ba mai iya kashewa,Saboda mugayen ayyukan da kukaaikata.”
5 “Ku yi shela a cikin Yahuza,Ku ta da murya a Urushalima, kuce,‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,‘Ku tattaru, mu shiga birane masugaru.’
6 Ku ta da tuta wajen Sihiyona!Ku sheƙa a guje neman mafaka,kada ku tsaya!Gama zan kawo masifa da babbarhalaka daga arewa.