Irm 40:5-11 HAU

5 Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi.

6 Irmiya kuwa ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa, ya zauna tare da shi da mutanen da suka ragu a ƙasar.

7 Sa'ad da shugabannin sojoji waɗanda suke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba,

8 sai shugabannin, wato Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan da Jonatan, 'ya'yan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, da 'ya'yan Efai, mutumin Netofa, da Yazaniya ɗan mutumin Ma'aka suka tafi tare da mutanensu zuwa wurin Gedaliya a Mizfa.

9 Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya.

10 Amma ni zan zauna a Mizfa, in zama wakilinku a wurin Kaldiyawa waɗanda za su zo wurinmu. Ku tattara inabi, da 'ya'yan itatuwa na kaka, da man zaitun, ku tanada su a gidajenku, ku zauna a garuruwan da kuka ci.”

11 Haka kuma Yahudawan da suke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu,