4 Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani,
5 sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.
6 Sai Isma'ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!”
7 Sa'ad da suka shiga birnin, sai Isma'ila ɗan Nataniya da mutanen da suke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.
8 Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba.
9 Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe.
10 Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.