18 “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’
19 “Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,
20 cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’
21 A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.
22 Domin haka yanzu fa ku sani takobi, da yunwa, da annoba, su ne ajalinku a wurin can da kuke sha'awar ku zauna.”