1 Sa'ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama'a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita,
2 sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan 'yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba!
3 Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.”
4 Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama'a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba.