1 Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab,“Kaiton Nebo, gama ta lalace!An kunyatar da Kiriyatayim, an ci tada yaƙi,An kunyatar da kagararta, an rusheta.
2 Darajar Mowab ta ƙare.Ana shirya mata maƙarƙashiya aHeshbon,‘Bari mu je mu ɓata ta daga zamanal'umma!’Ke kuma Madmen za ki yi shiru,Takobi zai runtume ki.
3 Muryar kuka daga Horonayim tanacewa,‘Risɓewa da babbar halaka!’
4 “An hallakar da Mowab,Ƙanananta suna kuka.
5 Gama a hawan Luhit, za su hau dakuka,Gama a gangaren Horonayim,Suna jin kukan wahalar halaka.
6 Ku gudu don ku tserar darayukanku,Ku gudu kamar jakin jeji.
7 “Kun dogara ga ƙarfinku dawadatarku,Amma yanzu za a ci ku da yaƙi,Kemosh zai tafi bautaTare da firistocinsa dashugabanninsa.