20 An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.
21 “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,
22 da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,
23 da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,
24 da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.
25 An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.
26 “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.