44 Wanda ya guje wa tsoro,Zai fāɗa a rami,Wanda kuma ya fito daga cikinrami,Tarko zai kama shi.Gama na sa wa Mowab lokacin dazan hukunta ta,Ni Ubangiji na faɗa.
45 “A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yangudun hijira suna tsaye ba ƙarfi.Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon,Harshen wuta kuma ya fito dagaSihon,Ta ƙone goshin Mowab daƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.
46 Kaitonku, ya Mowabawa!Mutanen Kemosh sun lalace,An kai 'ya'yanku mata da mazacikin bauta.
47 “Amma zan komar da mutanenMowab nan gaba,Ni Ubangiji na faɗa.”Wannan shi ne hukuncin Mowab.