35 Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Zan karya bakan Elam, indaƙarfinta yake.
36 Zan sa iska ta hura a kan Elam dagakusurwoyi huɗu na samaniya.Za ta watsar da mutane ko'ina,Har ba ƙasar da za a rasa mutuminElam a ciki.
37 Zan sa mutanen Elam su ji tsoronmaƙiyansu waɗanda suke nemanransu.Da zafin fushina zan kawo musumasifa,In sa a runtume su da takobi,Har in ƙare su duka,Ni Ubangiji na faɗa.
38 Zan kafa gadon sarautata a Elam,Zan hallaka sarkinta dashugabanninta.
39 Amma daga baya zan sa Elam kumata wadata.Ni Ubangiji na faɗa.”