60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila.
61 Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan.
62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’
63 Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis.
64 Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ”Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.