4 Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa matada yaƙi!Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakarrana!’Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, garana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.
5 Mu tashi mu fāɗa mata da dare,Mu lalatar da fādodinta.’ ”
6 Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ku sassare itatuwanta,Ku tula ƙasa kewaye daUrushalima,Dole in hukunta wannan birnisaboda ba kome cikinsa saizalunci,
7 Kamar yadda rijiya take da ruwagarau,Haka Urushalima take damuguntarta,Ana jin labarin kama-karya da nahallakarwa a cikinta,Kullum akwai cuce-cuce, da raunukaa gabana,
8 Ku ji faɗaka, ya ku mutanenUrushalima,Don kada a raba ni da ku,Don kada in maishe ku kufai,Ƙasar da ba mazauna ciki.”
9 Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Za a kalace ringin Isra'ila sarai,kamar yadda ake wa inabi,Ka miƙa hannunka a kan rassantakamar mai tsinkar 'ya'yaninabi.”
10 Da wa zan yi magana don in faɗakarda shi, don su ji?Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, suji,Ga shi, maganar Ubangiji kuwa tazama abin ba'a a gare su,Ba su marmarinta.